• Labaran yau

  'Yansanda sun bindige wasu masu garkuwa da mutane har lahira

  Hukumar 'yansanda na jihar Anambra ta bindige har lahira wasu masu garkuwa da mutane lamarin da ya kai ga tarwatsewar gungun mutanen sakamakon arcewa da sukayi yayin da suka ranta na kare.A wani bayani da kakakin hukumar Nkeiruka Nwode yayi,yace wadanda aka harbe sun sace wani mutum mai suna Nnamdi Ibru dan shekara 32 a wani gidan mai na garin Obosi ranar Laraba 11 ga Oktoba suka bukaci kudin fansa Naira Miliyan ashirin.

  'Yansanda na sashen harkar fashi da makami da garkuwa da bil'adama sun gudanar da ayyukan sirri da ya kai ga artabu da batagarin  yayin da batagarin suka farga cewa 'yansanda suna biye da sune sai suka buda wuta da bindigogi lamarin da ya kai ga halaka biyu daga cikin su yayin da wasu suka arce da raunukan harsashi wanda aka ceto kuma ya tsira da raunin harsashi a kafa da kafadarsa.

  An sami bindiga kirar gida guda daya a hannunsu da harsashin catridge guda biyu,wani gajeren bindiga ,wayan salula XQ 1000 da wani babur kirar Q-link wanda bai da rijista.

  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yansanda sun bindige wasu masu garkuwa da mutane har lahira Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });