• Labaran yau

  'Yansanda sun bindige dillalin wiwi har lahira (Hotuna)


  Jami'an 'yansanda a jihar Anambara sun harbe wani mutum har lahira bayan an sami buhu 15 na wiwi a cikin motarsa kirar Toyota camry.

  Lamarin ya faru a Tarzan junction na garin Nkpor akan hanyar Enugu-Onitsha ranar Juma'a 20 ga Oktoba.

  Bayanai sun nuna cewa 'yansandan sun tsayar da mutumin yayin da suke gudanar da aikinsu na binciken ababen hawa shi kuma ya ki daga bisani 'yansandan suka bishi daga Dennis memorial Grammar School (DMGS) 'yansandan sun kama shi a Tarzan junction sakamakon cinkoson ababen hawa.

  Sakamakon haka rigima ya kaure tsakanin mai motar da 'yansanda lamarin da ya zafafa har ya kai ga wani 'dansanda ya bindige mai motar wanda ya mutu nan take.

  Ganin haka ya sa wasu matasa suka kona wata motar ma'aikata amma direban ta ya tsira domin ya tsere , lamarin ya kara kazancewa bayan motar tilera ta take wani yaron mota da ya fado sakamakon rudani da ya auku.

  Hukumar 'yansanda ta jihar a wani jawabi da ta fitar ta bukaci jama'a su kwantar da hankali kuma su bi doka da oda tare da yin biris da jita-jita daga makiya zaman lafiya,hukumar ta kuma kara da cewa tuni aka kama 'yansanda da suka jawo wannan tashin hankali sakamakon kisan wadda aka ga buhunan wiwi a motarsa.
   Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yansanda sun bindige dillalin wiwi har lahira (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });