• Labaran yau

  'Yan fashi sun kashe 'yansanda 2 a banki sun arce da kudi da ba a san yawan su ba

  'Yan fashi sun kai hari a Bankin Skye Bank a garin Ifon na karamar hukumar Ose a jihar Ondo inda suka kashe 'yansanda biyu kuma suka sace kudi da ba'a tantance yawasu ba kawo yanzu.

  Rahotanni sun nuna cewa 'yan fashin sun kasa shiga bankin misalin karfe 3 na rana yanayi da ya sa suka yi amfani da nakiya suka fasa kofar tsaro na bankin kafin suka sami shiga ciki.

  'Yan fashin sun umarci jama'a su kwanta a kasa yayin da suka shiga wajen ajiyar kudi suka kwashe kudin.

  Majiyar mu ta shaida mana cewa 'yan fashin su akalla 15 sun iso Bankin ne a cikin motoci guda 3 dauke da mugan makamai kuma sun dauki kimanin minti 40 suna gudanar da harkar fashin a yanayi da ya jefa mazauna unguwar cikin firgici.

  'Yansanda guda 2 da aka kashe sun rasa ransu ne sakamakon musayar wuta da suka yi tsakanin su da 'yan fashin su 15. Babu dan fashi da aka kashe a lamarin.


  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: 'Yan fashi sun kashe 'yansanda 2 a banki sun arce da kudi da ba a san yawan su ba Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama