• Labaran yau

  Yadda 'dansanda ya yi wa matashi kazafin kasancewa kwarto sakamakon kishi (Hotuna)

  Idan baku manta ba a jiya mun kawo maku wani labari da hoton bidiyo wadda ake zargin wani mutun akan kwartanci da wata matar aure a jihar Edo,wani bayani da ya fito a yau daga hannun Lauyan wanda ake zargi ya nuna akasin haka.Lauyan ya nuna cewa shiri ne aka yi domin a cutar da wannan mutum ta hanyar kazafi kuma wanda ya shirya wannan mugunta wani Saje ne na 'yansanda mai suna Mr Nagbama Osakpamwan Eboigbe , A.K.A Smally wanda ke sashen Special anti robbery squad SARS.

  Lauya ya ce saje na 'yansanda Nagboma ya shirya da wasu batagari su 10 inda suka tafi wajen da Mr Ese Idehen yake shakatawa da abokansa,haka kawai saje Nagboma ya kama dukan Ese tare da batagarin da ya yo hayansu inda yake zargin Ede akan cewa yayi zina da matarsa daga bisani suka kaishi .caji ofis na Ugbor suka kulle shi har washegari.Bayan DPO ya saurari bayanin saje Nagboma da Ese DPO ya gargadi saje Nagboma akan kada ya kara amfani da caji ofis nasa ya ci zarafin wani ba bisa ka'ida ba kuma nan take ya sallami Ese.

  Bayanai sun nuna cewa matar saje Nagboma ta rabu da shi sakamakon fitinarsa da ta kasa jurewa,ganin tana gaisawa da Ede saje Nagboma ya hau kololuwar kishi lamarin da ya sa ya je ya aikata wannan sharri.

  Lauyan wanda aka ci zarafinsa Ese Idehan ya dauki matakin shari'a akan saje Nagboma bisa hurumin amfani da aikinsa ba bisa ka'ida ba,cin zarafi,karya da keta haddin bil'adama.


   Kalli yadda aka ci zarafin Ede a wanna faifen bidiyo:


  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com
  Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda 'dansanda ya yi wa matashi kazafin kasancewa kwarto sakamakon kishi (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });