• Labaran yau

  Wasu 'yan bautan kasa NYSC sun kirkiro na'ura ta musamman a B-kebbi (Hotuna)

  Wasu matasa masu yi wa kasa hidima na NYSC karkashin jagorancin Muhammed Okashat Bello 'dan asalin jihar Sokoto da Baminago Taminabe 'dan asalin jihar Rivers sun kirkiro wata na'ura mai kama da agogo da zai amfani jama'a ta hanyar yada sanarwa,nuna lokaci ko nishadantar da jama'a  har ma da kiran Sallah idan lokaci yayi wadda za'a iya girkawa a tsakiyar randabawal.

  Muhammed ya shaida mana cewa na'urar zata yi amfani ta fuska daban daban kamar kiran Sallah idan lokaci yayi,isar da sanarwa,nuna lokaci tare da ambaton ko karfe nawa ne hatta labarai daga kafar labarai da ake bukata.

  Shirin zai kasance samar da babban na'urar wadda za'a iya girka su a manyan randabawal da ake da su a cikin garin Birnin kebbi,ko kofar shigowa garin Birnin kebbi.Wani abin sha'awa shine yadda na'urar zata dinga amfani da karfin hasken rana wajen tafiyar da aikinta.

  Muhammed da Taminabe sun shaida mana cewa suna iya bakin kokarinsu domin ganin cewa Gwamnatin jihar Kebbi ta fahimci aikin fasaha da suke son su gabatar mata ta fuskar cewa wannan zai kasance tsani ga ababen fasaha irin wannan da Gwamnati da jama'ar jihar Kebbi za su iya amfana da su.

  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wasu 'yan bautan kasa NYSC sun kirkiro na'ura ta musamman a B-kebbi (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });