• Labaran yau

  Mutum 7 'yan gida daya sun mutu an ceto 2 sakamakon nutsewar jirgin ruwa a Yauri

  A kasa da mako biyu an sake samun nutsewar wani jirgin ruwa na kwale kwale a karamar hukumar Yauri na jihar Kebbi lamarin da yayi sanadin mutuwar mutane da asarar dukiya da suka nutse a ruwa.

  Hadarin jirgin ruwan ya faru ne a jiya da misalin karfe 8:00 na dare sakamakon bugawan iskan ruwan sama da ya rutsa da jirgin a kan ruwa.Lamarin ya shafi  mutum tara 'yan gida daya, biyu sun tsira.

  An ga gawar mutum bakwai kuma yanzu haka an Sallaci gawar mutum bakwai din a Garin  Rukubalo da ke karamar hukumar mulki ta Yauri. 

  Wadanda hadarin ya rutsa da su  dukansu 'diyan mal. Abdullahi rukubalo,sune kamar haka.

  Rayyanu Abdullahi ,Sa'adu Abdullahi ,Tukur Abdullahi ,Sani Abdullahi ,Zakiru Abdullahi,Maryam Abdullahi da Madina Abdullahi sai kuma Raiyanu da Sa'adu.

  Wadanda suka tsira a hadarin sune: Babangida Abdullahi da Yahuza Abdullahi.  Yayin da  ISYAKU.COM ya tuntubi shugaban hukummar bayar da agaji na gaggawa na jihar Kebbi kuma kakakin jam'iyar APC na jihar Kebbi Alh.Sani Dododo ya tababatar da faruwar lamarin ya kuma kara mana haske akan yiwuwar wasu matakai da hukumarsa ke shirin gabatarwa ga Gwamnatin jihar Kebbi domin tabbatar da lafiya da tsaron rayuka da dukiyan Al'umma a karamar hukumar Yauri dangane da matsalar hadarin jiragen ruwa.

  Yace matakan sune hana tukin jirgin ruwa bayan karfe shida na yamma, ware jirgin ruwa na mutane daban na daukan kaya daban, farfado da amfani da takarda da ke dauke da sunayen mutane da ke cikin jirgi da sunayen 'yan uwansu da lambar waya koda kaddara ta auku.Kassafa jirage zuwa aji-aji ma'ana manya daban kanana daban wadda hakan zai samar da tsari da zai kayyade irin adadin kaya da kowane jirgi zai dauka haka zalika zuwa aji na B ko C zai fayyace tare da ka'idance yawan kayan da jirage zasu dauka.

  Alh.Sani ya kara da cewa haka zalika za'a fayyace yadda jirgin kaya zai kasance a gaba wadda ke dauke da mutane kuma yana biye da shi a baya.Ya kara da cewa shirin zai hada da Sarakuna Dagacai,Hakimai tare da jami'an tsaro.

  Daga sani Twoeffect Yawuri da Sani Musa Saminaka


  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mutum 7 'yan gida daya sun mutu an ceto 2 sakamakon nutsewar jirgin ruwa a Yauri Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });