• Labaran yau

  Muguwar Mace! Matar da ta kashe diyar kishiya ta zuba wa miji ruwan zafi (Hotuna)

  An kama wata mata a kasar Zambia bayan ta zuba wa majinta tafasashshen ruwan zafi yayin da yake barci saboda ya tambayeta ko a ina ta kai diyarsa da ba'a gani ba. Charity Banda wadda ta amsa cewa ta kashe yarinyar 'yar shekara tara da ake nema watau diyar maigidanta kuma ta binne ta a kofar gidanta watanni goma da suka gabata.

  'Yansanda a garin Chisamba sun kai samame gidan domin kaddamar da binciken da ya kaisu ga tone kasusuwan yarinyar da Charity ta kashe bayan an shaida masu cewa Charity ta zuba wa mijinta ruwan zafi kuma ta tsere amma wasu matasa da suka shaida ta suka kamota suka kai ta gaban 'yansanda inda ta amsa kisan yarinyar kuma tayi wa 'yansanda bayani wurin da ta bizine yarinyar.


  Bayanai sun nuna cewa maigidanta ya tambaye ta inda ta kai diyar shi wadda uwargidan shi ta haifa amma sai Charity wadda ita ce Amarya ta ce ai ta kaita wata makarantar kwana,amma bayan da mai gidan ya yi bincike da ya kaishi ga gano cewa Charity ta yi mashi karya sai ya ce zai kai karar ta a gurin 'yansanda daga bisani Charity ta tafasa ruwan zafi a tukinya ta je ta watsa mashi a cikin barcin nashi sai ta ruga da gudu bayan ta ji yana ihu .

  Bincike ya nuna cewa wannan shine auren Charity na hudu kuma tsofaffin mazajenta mutuwa sukeyi a lokacin aurensu da Charity.  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Muguwar Mace! Matar da ta kashe diyar kishiya ta zuba wa miji ruwan zafi (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });