• Labaran yau

  Mai gadi 'dan shekara 57 yayi lalata da yara mata 'yan makaranta 54

  A kasar Afirka ta kudu wani tsoho 'dan shekara 57 wanda mai gadi ne a wata makarantar firamare a Orlando ta gabas ya fada hannun hukumomi bisa zargin yin lalata da yara 'yan mata guda 54 .

  Majiyar mu ta labarta mana cewa  mai gadin da aka sakaya sunansa yayi amfani da dama da ya samu na gadi a makarantar domin ya yi lalata da yaran kamar yadda wasu yara 'yan aji 2 da aji 6  suka shaida wa shugaban Makarantar.

  Wannan yasa shugaban Makarantar ta bukaci Malaman yaran su bincike su a cikin ajinsu,lamarin da ya haifar da sakamakon da ya nuna cewa tsoho mai gadi ya dade yana lalata da yara 'yan mata a Makarantar wanda adadinsu ya kai 54.

  Ana kyautata zaton wannan tsoho zai gurfana a gaban Kotu a Pretoria bisa tuhumarsa da lalata da kananan yara.

  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Mai gadi 'dan shekara 57 yayi lalata da yara mata 'yan makaranta 54 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama