• Labaran yau

  Karanta takardar wasiyya da 'yar shekara 16 ta rubuta kafin ta rasu (Hotuna)

  Aisha Ibrahim Umar wata budurwa ce 'yar shekara 16 da rasuwarta ya tayar wa mazauna unguwar Badarawa a jihar Kaduna hankali sakamakon yadda yarinyar ta rubuta wata takardar wasiyya wacce take dauke da kalamai masu ratsa zuciya.

  Marigayya Aisha ta rasu ranar Juma'a 27 ga watan Oktoba bayan 'yar gajeruwar rashin lafiya.

  A cikin takardar wasiyyar, Aisha ta roki iyayenta  gafara, 'yan uwanta,'yan makaratar ta da Malaman Makarantar da kuma kawayenta,

  Aisha ta bukaci masoyanta tare da jama'a su tsaya a kabarinta domin su yi mata addu'a bayan ta yi wafati.

  Daga karshe ta zayyana sunayen wadanda take son a aika masu da takardarta ta wasiyya.Ta kuma rubuta wanda take bi bashi kuma ta roke shi ya biya bashin.

  Mutane da dama yanzu haka suna dafifi a gidan su Marigayya  Aisha domin su karanta takardarta ta wasiyya mai ban tausayi da mamaki sakamakon darasi da ke ciki.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Karanta takardar wasiyya da 'yar shekara 16 ta rubuta kafin ta rasu (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama