• Labaran yau

  Iyaye sun dauke yaran su daga makarantu kan jita-jitan allurar monkeypox a Borno

  Rahotanni da suka fito daga jihar Borno a ranar Alhamis sun nuna cewa iyayen yara sun fantsama zuwa Makarantu domin su dauko yaransu bayan wani labari ya bazu a cikin garin Maiduguri inda ake zargin cewa wata kungiyar bayar da taimako tana yi wa yara 'yan makaranta allurar kamuwa da cutar kyandan biri watau Monkeypox.

  Wannan jita-jita yayi tasiri a kudancin Najeriya kafin a bankado shi yanzu zuwa Arewacin Najeriya wadda aka fara da jihar Borno.

  Babu wata hukuma da ta tabbatar da wannan lamarin kawo yanzu,amma tasirin rudani da jita-jitan ya haddasa ya bayyana a birnin Maiduguri sakamakon yadda labarin yayi saurin bazuwa inda aka gan cinkoson iyaye a kofar shiga makarantu alhali lokacin tashi bai yi ba.  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Iyaye sun dauke yaran su daga makarantu kan jita-jitan allurar monkeypox a Borno Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama