• Labaran yau

  An kama mutum 2 da suka yanka cikin wata mata suka cire jariri (Hotuna)

  Wasu mutum biyu sun fada hannun hukumomi a kasar Brazil bayan sun kashe wata mata mai dauke da juna biyu 'yar shekara 20 suka yanka cikinta suka zaro jariri da ke a mahaifan ta yanayi da ya kai ga mutuwar matar. Lamarin ya faru a São Sebastião do Uatumã  na jihar Amazonas .

  Bayanai sun nuna cewa Joelma Queila Santana da Silva mai shekara 22 tare da Alex da Silva Carvalho sun sami matar ce akan hanyarta na zuwa wajen ganin Likita a Itapiranga inda suka bukaci su je su dan huta daga bisani su ci gaba da tafiya.

  Yayin da suka isa wani gidan cin abinci sai suka dauke mata hankali yayin da Joelma ta saka mata maganin barci a lemun kwalba da take sha lamarin da ya sa tayi barci mai nauyi,ganin haka ya sa suka dauke ta suka kai ta wani daji inda suka yi amfani da wuka suka huda cikinta kuma suka zaro jariri a mahaifarta lamari da ya haifar da mutuwar matar nan take.

  Wasu mazauna unguwar Paz a yankin da aka fi sani da “Campo de Pelada Pimenta” sune suka gano gawar matar daga bisani suka shaida wa 'yansanda da suka kaddamar da bincike da ya kai ga kamo Joelma da Alex wadanda suka aikata laifin.

  Joelma ta shaida wa hukumomi cewa ta rudi Alex domin ya taimaka mata ne saboda saurayi ne da bai san inda Duniya ta dosa ba kuma tunda ita bata haihuwa tana son ta mallaki jaririn ne a matsayin nata,Rahotanni sun nuna cewa jaririn yana samun kulawa a wani Asibiti a garin Itapiranga.

  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kama mutum 2 da suka yanka cikin wata mata suka cire jariri (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });