An kama 'dan sandan da ya yi wa matashi kazafin kasancewa kwarto

Idan baku manta ba kwanakin baya mun kawo maku labarin wani saje na 'yansanda wanda ya shirya mugunta inda yayi wa wani matashi Ese Idehen kazafi cewa ya yi kwartanci da matarshi lamarin da ya kai ga cin zarafin wanda ake zargin a garin Benin na jihar Edo.

Wani sabon labari ya nuna cewa bayan gabatar da takardar koke daga Lauyan wanda aka ci zarafi ga Kwamishinan 'yansanda na jihar ta Edo,an kama saje Nagbama Osakpamwan Eboigbe kuma yanzu haka yana fuskantar tuhuma kamar kowane mai laifi.

Bayanai sun nuna cewa hatta 'yansanda da suka taimaka masa domin a kulle wanda ake zargin a cikin caji ofis su ma suna fuskantar shari'a na cikin gida bisa tsarin hukumar 'yansanda.



Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN