Yan sanda a jihar Ebonyi sun damke wani tsoho mai shekara 70 Simon Alobu bayan yayi wa yarinya 'yar shekara 7 fyade a Akpoha, na karamar hukumar Afikpo na Arewa a cikin jihar Ebonyi.
Majiyar mu ta labarta mana cewa Simon Alobu yana da mata 3 da yara 14 amma daya daga cikin matan ta mutu yayin da daya kuma ta tare a gidan danta.
Bayanai sun nuna cewa yarinyar tana fama da cutar wari sakamakon fyade da aka yi ta yi mata da ya hadu da matsalar rashin kulawa.
Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com