Mawaki Don Williams ya mutu

Shahararren Mawakin nan kuma marubucin wakoki dan jihar Texas na kasar Amurka Don Williams ya mutu yana da shekara 78.

Dan kungiyar Mawaka na Hall of Fame ya mutu ne bayan gajeruwar rashi lafiya kamar yadda na kusa da shi suka sanar, lamarin da ya jefa ilahirin 'yan Hall of Fame cikin damuwa da alhini.

Wannan ya farune shekaru biyu bayan Don Williams yayi murabus daga yin waka.

Wakokin Williams wadda shi kadai yake yinta yayin da yake kada jita galibi daga zaune a salo irin na Amurkawa 'yan asali ya kasance Mawaki da ya fi shahara a wannan saugar da ake kira Country Music.

Daga cikin wakoki da Duniya zata tuna da Don Williams kuma sun hada da 'Tulsa Time', 'Back in My Younger Days', 'You’re My Best Friend', 'Lord, I Hope This Day Is Good','Some Broken Hearts Never Mend' 

Ya mutu ya bar Matarsa Joy Bucher 'yar shekara 57 da 'ya'yansa biyu Gary Williams da Tim Williams.


Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN