• Labaran yau

  Kalli yadda aka kashe Hausawa a Abraka na jihar Rivers

  Da misalin karfe 10 na daren Juma'a wasu bata gari sun kai hari a wani matsugunin Hausawa a kasuwar Abraka a garin Asaba na jihar Rivers inda suka kashe mutum hudu tare da wata mata.

  Maharan sun jikata mutane da dama a harin da suka kai ta harbin mai uwa da wabi cikin duhun dare.

  Majiyarmu ta labarta mana cewa bayan harbe harbe da bindigogi maharan sun jefa bom a wani Masallaci yayin da wani jarumi Bahaushe ya yi kukan kura ya dauki bom din ya ruga waje ya jefar a wani rafi da ke kusa da Masallacin sai bom din ya fashe a rafi makin a Masallacin .

  Daga bisani 'yansanda da Sojoji sun kori 'yan ta'addan daga wajen da lamarin ya faru.  Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

  Hoto: nationalhelm 
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Kalli yadda aka kashe Hausawa a Abraka na jihar Rivers Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama