• Labaran yau

  Kalli abin da ya faru bayan matasa sun kashe Sojoji 4

  Rahotanni da ke fitowa daga jihar Bayelsa sun nuna cewa wasu matasa da ke dauke da makamai sunyi wa wasu sojojin Najeriya kwanton bauna inda suka kashe hudu daga cikin sojojin da ke kan hanyarsu ta dawowa daga wajen aiki a yankin Ekeremor mai sarkakiyar hanyoyin rafi bayan sun kammala aiki a yankin Letugbene ranar Litinin.

  Majiyarmu ta labarta mana cewa matasan da suka zarce yawan sojojin sun tasa keyar sojojin zuwa cikin daji bayan sun kwace bindigoginsu daga bisani suka buda masu wuta kuma suka arce da bindigogin sojojin.

  Tere Porri wani shugabane na wata kungiyar matasa ta kabilar Ijaw yayi Allah wadai da aukuwar lamarin yayin da wata majiya ta tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin.

  An gan sojoji da yawa sun shiga yankin da lamarin ya faru kuma jim kadan aka kula cewa wasu gidaje sun kama da wuta yayin da sojojin ke bincike sako-sako.
  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.

  Hoto: Nationalhelm
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli abin da ya faru bayan matasa sun kashe Sojoji 4 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });