• Labaran yau

  Hotuna: An raunata 'yan Kwankwasiyya a taron hawan Durbar a Kano

  Bayanai da ke fitowa daga jihar Kano sun nuna cewa an sammi hatsaniya tsakanin magoya bayan Gwamna Ganduje da na tsohon Gwamna Rabiu musa Kwankwaso wadda aka fi sani da suna Kwankwasiyya.

  Rahotanni sun nuna  cewa lamarin ya farune a wajen hawar Darbur a kofar Mai Martaba Sarkin Kano ranar Assabar yayinda wasu da ake zargin cewa magoya bayan Gwamnan Kano Ganduje suka dira a wajen kallon Darbur inda suka afka wa 'yan Kwankwasiyya da duka da itace,wukake da sauran mugan makamai.

  Rahotannin sun kara da cewa cikin wadanda ake zargin an raunata harda tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Kano lokacin Rabiu Kwankwaso (SSG) Sulaiman Bichi,Kanin Rabiu Kwankwaso Dr Adamu Yunus Dangwani da Comrade Aminu Abdulsalam wadanda tsofaffin Kwamishinoni ne a zamanin Rabiu Musa Kwankwaso.

  Dr Dangwani ya shaida wa Daily Trust aukuwar lamarin.Yanzu hake akwai zarge-zargen cewa wani dan majalisar Dokoki na jihar Kano Honourable Baffa Babba Dan Agundi shine ya umarci matasa su yi wannan aika-aikan,amma a nashi jawabin Honourable Baffa Babba Dan Agundi ya musanta kasancewa da hannu a wannan aiki inda ya kara da cewa "Babu yadda za'ayi dan majalisa mai wakiltar jama'a ya bayar da umarni a yi tashin hankali,kuma idan har abinda Kwankwasiyya ke fada gaskiya ne ai sai su gabatar da hujja"

  Majiyar mu ta shaida mana cewa an garzaya Asibitin Aminu Kano inda aka yi wa wadanda aka raunata magani daga bisani aka sallame su.
  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotuna: An raunata 'yan Kwankwasiyya a taron hawan Durbar a Kano Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });