• Labaran yau

  'Dan Luwadi ko 'dan kishin kasa ? - Isyaku Garba

  Yau  2 ,Muharram,1439AH daidai da Juma'a 22 ga watan Satumba 2017 wadda ranace mai tarin albarka kasancewarta rana ta farko a watan farko a kalandar Musulunci.Ina son inyi amfani da wannan dama domin in shaida wa Duniya abin da ya faru a shekaru da suka gabata wadda sakamakon haka wadansu makiya gaskiya da son girka kananan maganganu suke amfani da shi domin su aibanta mutunci da darajan bayin Allah da basu da hakki akansu.

  Da farko dai ina son in shaida wa Duniya cewa ni Isyaku Garba ba dan Luwadi bane kamar yadda wasu mutane ke gulma akai. Na fuskanci wulakanci,an ci zarafi na,an kaurace mini,an zage ni babu abinda ba'a yi mini ba amma a garin Birnin kebbi kawai ne domin wasu sunce Isyaku dan Luwadi ne babu bincike wasu kuma sun yarda.

  Ga abinda ya faru wadda ya samo asali tun 1986 a lokacin da muke makarantar Sakandare a Haliru Abdu.

  A farko zangon karatu 1986 wata matsala ta bullo a barikin Soja na garin Birnin kebbi wadda ni kaina mahaifi na Soja ne a waccan lokacin inda aka sami wasu mutane daga cikin gari sun bata wasu 'ya'yan sojoji ta hanyar luwadi lamarinda ya haifar da bincike mai tsanani a cikin barikin kuma daga bisani aka samar da tsarin da ya janyo mu a ciki domin ba nikadai ne aka zaba ba domin tafiyar da shirin.

  Hukumomin soji a waccan lokacin karkashin jagorancin sashen leken asiri na soja DMI ko Army intelligence sun samar da horo a lamari da ya kai ga zaban yara uku ciki har da ni Isyaku Garba daga Makarantar Haliru Abdu ,sai makarantar jeka ka dawo na Abdullahi Fodio wadda su ne makarantun da aka fi samun 'ya'yan sojoji .

  Aikin mu a waccan lokacin shine mu shiga 'yan uwanmu yara domin mu gano ko su waye ke irin wannan harka ta luwadi mu kuma mu kai rahotu ga jami'an Army Intelligence a bariki .

  Wannan shirin ya ci gaba har zuwa 1987 wadda daga bisani wata rana aka gayyace mu inda muka je barikin soja a cikin makarantar Firamare na barikin watau Army Children School aka ware aji daya inda muka gan wasu fuskoki da bamu saba gani ba bayan hafsoshin soja kuma suka sanar da mu cewa daga ranar nan an daukaka matsayin mu zuwa informants watau masu bayar da bayanan sirri ga tsarin hadin guiwa tsakanin sashen leken asiri na soja da hukumar SSS akan lamarin luwadi a garin Birnin kebbi gaba daya.

  A waccan lokacin an fara bamu alawus a kowane wata kuma aka fara ba mu horo na tsari da salon leken asiri da yayi daidai da lokacin mu.An tsara mana yadda zamu dinga zuwa dakin karatu Library domin mu karanta darasi kafin Malami ya zo aji ya karanta mana saboda kada a bar mu a baya sakamakon ayyukan da aka sanya mu.

  1988 an kara daukaka matsayin mu zuwa Agents kuma aka canja mana salon suna da za mu dinga amfani da shi wajen rubuta rahotu bisa ga yadda muke bayar da rahotu da farko ta hanyar zuwa ka yi wa ubangidanka bayani wadda muke kira X Principal ni kuma aka bani suna HA1 akwai HA2 da HA3.Makarantar Abdullahi Fodio kuma akwai AF1 zuwa AF3 haka zalika an sanyo Government science secondary school daga baya amma su ana kiransu SUB1 zuwa SUB3 domin horon su bai kai namu ba su sun shigo ne a 1988 mu kuma tun 1986.

  Daga cikin ayyukan mu akwai :

  1- Gano dan luwadi a cikin al'umma
  2- Gano gidansa da wajen aikinsa ko wajen sana'arsa
  3- Yaranda da yake wannan hulda da su
  4- Manya daga cikin abokan huldarsa ta wannan fanni
  5- Dana masa tarko ta yadda za mu kama shi
  6- Tsara fallasa shi ba tare da sanin abinda ake ciki ba
  7- Samar da hujjoji da zasu kai ga hukunta shi
      Da dai sauransu.

  A 1989 an daukaka mukami na zuwa H1+ ma'ana nine jagora ga sauran Agents saboda na kai aji na kusa da karshe.A wannan lokacin ne na gamu da babban kalubale da ya kai ga matsayin da ake ciki a yanzu domin a wannan matakin an tsara mana abinda ake kira Relentless Pick watau sai kawai ka zabi yaro daga cikin dalibai a Makaranta ko abokin ka a cikin gari ka bi wajen wadda aka tabbatar dan luwadi ne sakamakon huldar su zaka fahimci ko sun wayi juna a tsarin ,daga bisani sai ka fadada bincike a asirce.

  Haka zalika mataki na Target Penetration wadda zai baka dama ka je har gidan dan luwadi harma za ka iya kwana a gidan ba tare da ka yarda anyi luwadin da kai ba sakamakon haka zai sa ka gane idan akwai yaron da ake kwana da shi a gidan domin aikata luwadi.

  Mataki na karshe shine shirye shiryen mika ragamar aiki ga na baya da mu tare da zakulo hazikan yara da za su maye gurbin mu.Wannan mataki shine ya bamu dama mu tona asirin duk wani dan luwadi wadda dama mun sani suna aikatawa amma bamu fallasa su ba domin kada mu rasa madogara na ci gaba da samun bayanai .Idan shugaban dalibai (Head boy) na Makarantar mu Haliru Abdu a waccan lokaci bai manta ba ni da kaina na fallasa masa da sauran 'yan ajin mu lamarin wani dan luwadi da aka aiwatar da hukunci na mu manya a makarantar a bayan Raka.

  Daga bisani mun gamu da matsala irin na cin amana, domin wasu yara guda biyu da na sa sunayensu a cikin tsarin tafiyar kuma daga bisani basu sami cin jarabawan gwaji da zai tabbatar da su a shirin ba sai suka dinga zagayawa a Birnin kebbi da Makaranta suna cewa ai ni dan luwadi ne,a bangare daya kuma wasu da muka bayar da shaida a caji afis akan su 'yan uwansu ko 'ya'yan su da muke makaranta tare suka fara zagayawa a garin Birnin kebbi suna cewa ai Isyaku Garba dan luwadi ne domin su yi rigakafi kafin mu mu furta haka akan 'yan uwansu.

  Daga karshe lamari dai kamar yadda aka yi mana alkawari ni HA1+ na zama cikakken jami'in DSS har nayi ritaya HA2 da HA3 kuma har yanzu suna hukumar leken asiri na soja Defence Intelligence Agency DIA na sami labari a 1995 cewa AF1 yana hukuman leken asiri na Najeriya National Intelligence Agency NIA saura AF2, AF3 da SUB1 zuwa SUB3 bani da labarinsu har yau.

  A cikin garuruwa da unguwanni da na zauna a Arewacin Najeriya babu gurin da aka taba ji ko aka alakanta ni da Luwadi sai a garin Birnin kebbi.Za ka iya bincikawa a wadannan guraren SOKOTO-Gwuiwa lowcost,Gwuiwa gari,Old Airport,Mabera jelani da Gidan Igwai. KANO-Dala,Brigade,Kwandila Estate hanyar gidan Zoo, 'Yan kaba da Giginyu. JIGAWA-Dutse da Mai gatari. ABUJA-Garki 2,Garki Village,Asokoro,Nyanya,Maraba,Maitama,Npape,Mambilla Barracks da Life Camp.Kadan kenan daga gurare da na zauna a Arewa sai ka bincika zamantakewa ta da sauran Mutane dangane da ko ni dan Luwadi ne.

  Ina son in yi amfani da wannan dama in shaida wa Duniya cewa banyi nadama akan aiki da nayi wa kasata ba kuma har abada ba zan yi nadama ba,ina kuma kira ga jami'an ayyukan asiri kamar DSS,NIA,DIA da sauran jami'an tsaro irin su CIB,CIID da sauransu akan cewa a ko da yaushe idan kun sami kanku a cikin ayyukan sirri da ya shafi irin wadannan mutane na Luwadi ko abinda ya shafi haka ,ku tabbata kun ajiye Record na zamani saboda zamani ya canja mutanen nan sun shahara wajen munafunci.

  Ina kallo kiri kiri dan luwadi dan gidan dan luwadi jikan dan luwadi amma yana kirana dan luwadi.Na kalubalanci duk dan makarantar mu ta Haliru Abdu a garin Birnin kebbi idan ya san lallai ya shaida kuma ya tabbata cewa ni Isyaku Garba dan Luwadi ne don Allah ya zo mu bashi dama yayi bayani wa Duniya.Ka zo da ranan wata ko shekara ko su waye suka kamani da laifi ko su waye suka yi mini hukunci,na 'yan uwana dalibai,ko hukumar Makaranta ko jami'an tsaro.Idan ba haka ba kashedin ku,kazafi ne kuma ba mamaki za ka haifi dan Luwadi a gidanka.

  Ina kira ga Iyalina da dukkannin 'ya'ya na ,Kawunnai na,'yan uwana ,duk wani mutumin kasar Zuru,masoya na a garin Birnin kebbi,Surukkaina,Makwabta na, akan cewa kazafi ne aka yi mini na Luwadi kuma daga zuriyar 'yan Luwadi amma ni Isyaku ba dan Luwadi bane kuma ina son ku san haka.

  Ina godiya ga Allah da ya bani ikon bauta wa kasata ta fannen ayyukan sirri da Janar Ibrahim Badamasi Babangida da lokacin shi ne aka bani aiki da Hukumar ayyukan sirri na cikin gida na Najeriya DSS.


  Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Dan Luwadi ko 'dan kishin kasa ? - Isyaku Garba Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });