• Labaran yau

  An sami hargitsi tsakanin Hausawa bayan kisan mai Suya a Lagos

  A ranar Juma'a da ta gabata a unguwar Okokomaiko a garin Lagos an sami wata matsala da ta taso tsakanin  Bashiru Ahmed 'dan Sarkin Hausawa na Okokomaiko da wani mai Suya.Wata majiya ta labarta cewa wani ya rada wa dan Sarkin Hausawan cewa shi mai Suya yayi masa dariya yayin da ya fada a wani gwata lokacin da yake ketarawa.

  Majiyar ta ci gaba da cewa dan Sarkin Hausawan Bashiru Ahmed  da abokansa sun juyo sai suka zubar masa da Suyarsa a kasa lamarinda ya sa mai suyan ya je har gida Sarkin Hausawan domin yayi kara akan abinda dansa yayi masa. Amma sai wasu abokan 'dan Sarkin Hausawan suka harbe shi suka wuce abinsu lamarin da yayi sanadin mutuwarsa.

  Daga bisani majiyar ta ci gaba da cewa abokan mai Suya sun hada kansu inda suka bi daya daga cikin abokan 'dan Sarkin Hausawa wadda yana cikin wadanda suka kashe mai suya shi ma suka kashe shi a kusa da Alaba Rago daga bisani suka koma gidan Sarkin Hausawan suka kona bangaren gidan kurmus.

  Wasu manyan jami'an tsaro a jihar ta Lagos sun kawo dauki inda suka gudanar da wani taro na shugabannin al'umma na yankin domin kaucewa yiwuwar harin ramuwar gayya ko daukar fansa.
   

  Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An sami hargitsi tsakanin Hausawa bayan kisan mai Suya a Lagos Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });