• Labaran yau

  "Zuciyar dan adam sinadari ne na tsafin neman dukiya" - Matsafi

  Rundunar 'yansanda na jihar Ogun a ranar Alhamis ta gabatar wa manema labarai da wani mutum mai suna  Bakare Olalekan wanda aka kamashi  da zuciyar bil'adama guda uku wanda ake zargin cewa ya sayo su  akan kudi Naira dubu goma N10.000.

  Olalekan ya amsa  cewa lallai shine ya samo zuciyar ta bil'adama kuma wani abokinsa ne ya bukace shi cewa ya samo zuciyar dan adam saboda dalilai na tsafi da zai kaishi ga samun nassara da dimbin dukiya a rayuwarsa amma zuciyar bil'adama shine babban sinadari da ake bukata a lamarin.

  Wanda ake zargin yana cikin mutum 55 da Kwamishinan 'yan sanda na jihar Ogun Ahmed Illiyasu ya gabatar da su  wa manema labarai wadanda suka aikata laifuka daban daban a fadin jihar.

  Kwamishina Illiyasu ya kara da cewa Bakare Olalekan yana cikin gungun mutum hudu da aka kamasu bisa zargin kashe wata budurwa yar shekara 16 Olayinka Adebayo a watan Agusta na bara.

  Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: "Zuciyar dan adam sinadari ne na tsafin neman dukiya" - Matsafi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama