• Labaran yau

  'Yan fashi a Katsina sunyi wa wani dan kasuwa fashi a Masallaci

  Yayin da aikata ta'addanci ke ci gaba da yaduwa musamman a kasar Arewacin Najeriya a birnin Katsina kuwa wasu mutum 7 ne suka bayyana a gaban wata Kotu bisa zargin fashi da makami.

  Bayanai sun nuna cewa mutanen sun kai wa wani dan kasuwa Alh.Hassan Ishaku farmaki ne a wani Masallaci da ke unguwar Rafin dadi a cikin garin Katsina inda suka kwace kayaki da aka kiyasta akan N43,000 .

  A karshen makon da ya gabata, ‘yan sandan suka gurfanar da su a kotun majistare da ke jahar, inda mai gabatar da kara yace abunda suka aikata ya sabawa sashe na 96(2),(a) da 306 na kundin Dokar ‘Penal Code’ da dokar fashi da rike makamai.

  ‘Yan fashin sun hada da: Aliyu Arab, wanda aka fi sani da kolo; Amadu Suleiman, wanda aka fi sani da Jimmy; Murtala Ghali, wanda aka fi sani da Nasara; Hassan Lawal, wanda aka fi sani da Rugged; sai Ibrahim Haruna, wanda ak fi sani da Baba Iro.

  Sai sauran, Bishir Ishak, wanda aka fi sani da Tinkiya; da Muntari Saidu, wanda aka fi sani da Maisalati.
  Dukkaninsu mazauna yankin Mobil Rafindadi Quarters ne a Katsina.

  Yanzu haka kotu ta bada umarnin a tsare su a gidan yari har ranar 23 ga watan Agusta yayin da za a saurari karar.
  Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yan fashi a Katsina sunyi wa wani dan kasuwa fashi a Masallaci Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });