• Labaran yau

  Ya kashe dan adam bisa zargin satan ayaba

  Moses Erutuya wani manomi ne wanda ke da gonar Ayaba a kauyen Odhigili a jihar Edo,Moses ya kama wani da yake zargin cewa barawo ne mai suna Jonathan da ya dade yana yi masa satan Ayaba a kodayaushe idan lokacin girbe Ayaba yayi.

  Bayan Moses ya kama Jonathan barawon ayaba surki 35 sai yayi amfani da wani itace ya buge Jonathan a kai lamarin da ya janyo mutuwarsa nan take.

  The Nation ta ruwaito cewa Kwamishinan 'yansanda na jihar Edo CP Haliru Gwandu ya tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin ya kara da cewa rundunarsa zata gabatar da wanda yayi kisan a gaban Kotu.


  Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Ya kashe dan adam bisa zargin satan ayaba Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama