• Labaran yau

  Kashedin makiya Buhari da suke son ya mutu - Lauretta Onochie

  Wata mai taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin watsa labarai  Lauretta Onochie ta caccaki Fani Kayode da Ayodele Fayose a matsayin mutane masu fatar mutuwa ga shugaba Muhammadu Buhari da yadda suke furta kalamai na rashin mutunci da ragowa ga shugaba Buhari wadda ya girme su a shekarun zaman Duniya.

  Lauretta Onochie ta yi bayani cewa “Kwanakin baya wani hadimin Fayose, Lere Olayinka ya rubuta a shafin sa na yanan gizo cewa shugabankasa ya mutu.

  “Mun san ta inda abubuwan nan suke fitowa kuma mun san dalilin da yasa suke haka, hukuma tana bin su.
  “Amma Buhari bai damu da su ba, idan ka karya doka, dole doka ta cika, Wannan shine batu.

  “Sunce wai yan jam’iyyar PDP ne kadai ake hukunta wa, dalili shine ba mu a cikin gwamnatin da ta gabata, kuma bamu saci kudi ba, ta yaya hukuma za ta biyo mu.

  “Na fada sunayen su kuma bana tsoro. Burin su shine su ji ance ya mutu amma Allah ya fi su.

  Jawabin Onochie ya zo ne bayan Buhari ya dawo daga Landan, bayan ya kwashe sama da kwanaki 100 wajen ganin likitocin sa .


  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kashedin makiya Buhari da suke son ya mutu - Lauretta Onochie Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });