• Labaran yau

  Dan sandan bogi ya saci wayoyin salula 2 ya ba karuwarsa 1

  Rundunar 'yan sanda na jihar Ogun ta damke wani matashi mai suna David Fashina da yayi shigar sojan gona sanye da tufafin damara na 'yan sanda wadda yayi amfani da wannan damar ya sace wayoyin salula guda biyu daga wajen wani mutum kuma ya ba karuwarsa daya shi kuma ya je ya sayar da dayan akan N90.000.

  Jaridar Tribune ta ruwaito cewa wani Likita mai suna Dr Eniola shene ya kai kara wa 'yansanda cewa wasu mutane biyu daya sanye da kakin 'yansanda sun yi masa fashi inda suka kwace masa wayoyin salularsa guda biyu.Lamarin da yasa rundunar ta wakilta wani safeto wadda ya fara bicike da ya kai ga kama batagarin.

  Wanda ake zargin ya amsa laifinsa a gaban 'yan jarida yayinda aka gabatar da shi a bisa laifin da ake tuhumarsa ya kara da cewa kakin yan sanda da yayi amfani da shi kakin mahaifinsa ne wanda tsohon dan sanda ne.

  Kwamishinan 'yansanda na jihar Ahmed Iliyasu ya shaida wa manema labarai cewa rundunasa zata gurfanar da Fashina a gaban Kotu.   
  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dan sandan bogi ya saci wayoyin salula 2 ya ba karuwarsa 1 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });