"Boko haram ta yanka 'yan garin Aliero 42 tsohon labari ne" - Musa Hassan Kalgo

Bayan karafe korafe da dubannin masoyan shafinmu sukayi dangane da labarin da muka wallafa wadda ke da asali da shafin Daily Post akan lamarin Manoma 'yan asalin garin Aliero da boko haram ta yanka su bisa wannan maudu'in ISYAKU.COM  ya binciko cewa ba haka lamarin yake ba domin kafafen labarai da suka fara wallafa labarin basu fahimci kalaman da mai girma Gwamnan Kebbi ya fada bane yayin da yayi bayani ga wakilan tawagar majalisar dinkin Duniya ranar Laraba a Birnin kebbi.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Kebbi Alh.Musa Hassan Kalgo ya kara mana haske game da lamarin a bincike da ya kaimu ga magana da shi a wayan salula,Alh.Musa ya shaida mana cewa babban kuskure ne wasu kafafen watsa labarai suka tafka wajen gaya wa Duniya abinda mai girma Gwamnan jihar Kebbi ya fada game da lamarin.

Ya fayyace mana cewa Mai girma Gwamna yana bayani ga tawagar majalisar dinkin duniya ne akan irin matsaloli da jihar Kebbi ke fuskanta ta bangaren tsaro daya daga cikin dalilai da ke haifar da wahala wajen samun cikakken nassara a aikin yin rigakafin cutar polio ga yara kanana.Daga cikin misalan da Gwamna Atiku Bagudu ya bayar har da na yadda wadanda rikicin boko haram  ya shafe su a yankin Borno kuma suka yi gudun hijira zuwa cikin jamhuriyar Nijar daga bisani hukumomi a Nijar suka taso keyarsu zuwa Najeriya ta jihar Kebbi wadda hakan ya haifar da damuwa akan samun nassara a rigakafin yara kanana.

Haka zalika "Mai Girma Gwamna Atiku Bagudu ya bayar da wani misali inda yace bayan jihohin Borno,Yobe da Adamawa babu wata jiha da ta dandana azaba daga hannun kungiyar boko haram kamar jihar Kebbi kuma a bisa wannan gaban ne Gwamna Atiku ya tuno yadda a shekarar bara 'yan kungiyar boko haram suka yiwa wasu manoman albasa 'yan asalin garin Aliero su 42 yankan rago a jihar Borno" .

Alh.Musa Hassan Kalgo ya kara da cewa "wannan baya nufin cewa sabon lamarine ya faru,labari ne Gwamna ya bayar da lamarin da ya faru a bara ba wai sabon lamari ne ba".Ya kuma bukaci kafofin watsa labarai da suka rubuta wannan labarin cikin kuskure su gyara yayin da su daga Gwamnati zasu fitar da sanarwa akan wannan kuskuren fahinta da aka samu dangane da kalaman mai girma Gwamna Atiku Bagudu ranar Laraba.


Isyaku Garba - Birnin kebbi

Shafin mu na Facebook
 https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN