• Labaran yau

  "APC ta ruguje kyakkyawar tsari da PDP tayi na shekara 16" - Ben Obi

  Sakataren jam'iyar 'yan adawa na PDP na kasa Ben Obi ya cewa jam'iyar APC mai mulki ta ruguza kyakkyawar tubali da tsari da PDP tayi wa 'yan Najeriya na tsawon shekara 16, Obi ya shaida haka ne a yayin wani taron wakilan 'yayan jam'iyar wadanda ba zababbu ba da aka gudanar a ranar Asabar a Abuja.

  Obi ya kara da cewa "bayan APC ta ruguje tubali da kyakkyawan tsari da PDP tayi har yanzu APC bata da abinda zata nuna wa 'yan Najeriya".

  Haka zalika Obi ya kara da cewa "duk da mawuyacin hali da 'yan Najeriya suka sami kansu a ciki,har yanzu mutane suna nuna kauna ga jam'iyar PDP kamar yadda aka shaida a wasu zabuka da aka maimaita kuma jama'a suka zabi PDP. Yayin da mu PDP muka dukufa wajen kai sako da dandanon Dimokaradiyya ga talakkan Najeriya ita APC dukufa tayi wajen tsintar kalilan mutane da tsari maras amfani ga jama'a"
  Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: "APC ta ruguje kyakkyawar tsari da PDP tayi na shekara 16" - Ben Obi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama