• Labaran yau

  An kore 'dan sanda daga aiki wanda ya bari mai laifi ya tsere

  Rundunar 'yansanda na jihar Rivers ta kore Sergeant Johnbosco Okoroeze daga bakin aikin 'yan sanda bisa zarginsa da hada baki kuma ya saki mai laifi da gangan.Sergeant Johnbosco yana sashen binciken manyan laifuka na rundunar (SCIID) kafin korarsa daga aiki.

  Sergeant Johnbosco Okoroeze shine ke kula da bincike akan wani matashi da ya kashe diyar makwabcinsa a Port Harcourt bayan yayi mata fyade kana ya kwakwale idanunta ya kuma cire wasu sassa na jikinta kafin ya fada hannun yansanda lamarin da ya kaiga bincike da aka wakilta Sergeant Johnbosco Okoroeze.

  Daga bisani aka sanar cewa mai laifin ya tsere daga hannun 'yansanda lamarinda yasa Kwamishinan 'yansanda na jihar Rivers CP Ahmad Idris ya bayar da umarnin kama mai bincike akan lamarin watau Sergeant Johnbosco Okoroeze wadda bayan takaitaccen bincike na cikin gida aka kore shi daga aikin 'yan sanda kuma aka gabatar da shi a gaban Kotu ba tare da bata lokaci ba.

  Rahotanni sun nuna cewa  Sergeant Johnbosco Okoroeze yayi ta kuka babu kakkautawa yayin da aka gabatar da shi a gaban wata Kotun Majistare da ankwa a hannayensa yana cewa "wayyo Allah me ke faruwa da ni ,miye na aikata haka,don Allah a kira mini mata ta" lamarin da ya sa Alkalin Kotun Sokari Andrew-Jaja ya gargade shi.

  Bayan sauraron karar da rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta shigar akan korarren 'dan sandan ,Alkalin Kotun ya dage shara'ar zuwa ranar September 14, 2017 yayinda aka ci gaba da tsare wadda ake zargin a hannun hukumar 'yan sanda na jihar ta Rivers.  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kore 'dan sanda daga aiki wanda ya bari mai laifi ya tsere Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });