• Labaran yau

  Yara sunyi hawayen jini akan Uwa ta shafa masu barkono bayan ta yi masu duka

  Duniya sha kallo,a yayin da wasu ke matukar rokon Allah domin ya basu yara na haihuwa,watakilan saboda suna da matsalar rashin haihuwa,kuma wasu ma zasu iya yin iyakacin abinda zasuyi matsawar dai zasu sami yaro ko yarinya da zasu kira su da suna baba ko mama.

  Amma a wajen wata mata a unguwar Ajah a garin Lagos ba haka abin yake ba ,domin cikin yaran da Allah ya bata idan bancin gallazawa,tursasawa da bala'i babu abinda yaranta ke gani daga gurinta.

  Makwabta sun shaida cewa matar a kulli yaumin tana duka,zagi ,tursasawa da wulakanta wadannan yaran.

  Wannan matar bayan ta likida wa yaran su biyu na miji da mace dukar tsiya,ta kuma shafa masu yaji a fuska wanda ya haifar da zubar hawayen jini daga idanun yaran da basu wuce shekaru biyar ba .

  Bayanai sun nuna cewa makwabta sun kai karar wannan matar ga hukumar kula da harkar yara ta jihar Lagos domin a tauki mataki.
  Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb =  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.=  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. = Shiga shafinmu kai tsaye  www.isyaku.com   Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Yara sunyi hawayen jini akan Uwa ta shafa masu barkono bayan ta yi masu duka Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama