• Labaran yau

  Yadda aka kashe wani Soja a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna

  An sami gawar wani Soja da ba'a fadi ko waye ba wanda aka kashe a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

  Bayanai sun nuna cewa Sojan ya tuko motarsa daga Abuja yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna  sai tayar motarsa tayi faci.

  Sojan ya fito yayi ta kokari saboda ya sami taimako amma da yake babu wanda ya taimaka masa sai ya hau kan motarsa domin ya dan huta.Daga bisani barci ya kwashe shi.

  Wata majiya ta ce bayan Sojan yayi barci ne sai wasu matasa da ba'a san ko su waye ba suka fito daga daji suka sassare shi da adda kuma suka tsere.

  Babu wani bayani  daga hukumomi dangane da wannan lamari kawo yanzu.


  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Yadda aka kashe wani Soja a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama