• Labaran yau

  Maigida yace ta bace,amma an gano gawarta a cikin gidansa har ta fara rubewa

  Kwanaki hudu bayan an sanar da bacewar wata mata mai suna Naja'atu wanda matar wani Malamin Makaranta ne da ke koyarwa a Kwalejin Ilimi da ke Maru a cikin jihar Zamfara mai suna Mallam Yakubu Maradun an gano gawar matar a gidan ta bayan ta fara rubewa.

  Bayanai sun nuna cewa yanzu haka Malam Yakubu yana taimaka wa 'yansanda wajen bincike akan musabbabin mutuwar matarsa a gida bayan ya sanar cewa Naja'atu ta bace bayan ta je Banki domin ta cika takardun BVN a Gusau kwanaki hudu da suka gabata.

  Wata majiya ta labarta mana cewa wani dan uwan Naja'atu ne yaje gidan Malam Yakubu domin yayi ta'aziyya,amma sai ya fuskanci wani mumunar wari yana  busowa daga wani daki,kuma da ya tambayi Yakubu ko meye musabbabin wannan warin sai Yakubu ya shaida masa cewa ai wani masai ne ya fashe shi ya haifar da warin.

  Amma shi dan uwan Naja'atu bai yarda ba lamarin da ya kai ga bude wani daki daga inda warin yafi busowa kuma nan take aka ga ashe Naja'atu ce a mace har ta fara rubewa kuma aka lullube ta da wani tsumma.

  Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda na jihar Zamfara  DSP Shehu Muhammad ya tabbatar da aukuwar lamarin ya kuma ce ana ci gaba da bincike.  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Maigida yace ta bace,amma an gano gawarta a cikin gidansa har ta fara rubewa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });