• Labaran yau

  Dan Taxi ya kashe tsohon Ambasada ya gudu da Motar sa kirar SUV

  Yansanda a birnin Abuja sun damke wani matashi mai suna Lamidi Sikiru wanda ake zargi da kisan tsohon Ambasadan Najeriya a kasar Afrika ta kudu  Mr.Ngam Nwachukwu.

  Majiyar mu ta labarta mana cewa lamarin ya faru ne bayan wata rana Ambasadan ya tare motar Taxi da Sikiru yake tukawa ,a yayin da suke cikin tafiya sai Ambasadan ya gaya wa Sikiru cewa yana da wata mota SUV wanda take da wata 'yar matsala na kanikawa,sai Sikiru yace masa ai  yana da wani dan uwa wanda ke gyaran irin wannan motar.

  Ambasada ya bukaci Sikiru ya dawo washe gari,da Sikiru ya shigo gidan Ambasada sai ya tarar da shi yana cin abinci kuma yayi mashi bisimilla,amma mugun naka marmakin ya ci abinci sai ya zagayo  ya zaro almakashi ya dinga daba wa Ambasada wannan almakashin a wuyarsa har sai da rai yayi halinsa.

  Daga bisani Sikiru ya cire talabijin Plasma,na'urar kida da sauransu, daga karshe ya sanya kayakin a cikin motar SUV na marigayin kuma ya fice dasu daga gidan ya tafyi ya sayar da motar a kan N1.430milion,plasma  da kayan kida kuma ya sayar da su N38.000.

  Tuni dai yansanda suka zurfafa bincike a yayin da wannan jawabin ya fito daga bakin Sikiru shi da kansa lokacin da yake yi wa 'yansanda bayani.
  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Dan Taxi ya kashe tsohon Ambasada ya gudu da Motar sa kirar SUV Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama