An nada Alh.Garba Bube a matsayin Hakimin Garin Saini | isyaku.com

A yau Asabar 8/7/2017 mai girma Dan Galadima Abubakar Arzika Kalgo ya nada Alh.Garba Bube a matsayin Hakimin Garin Saini da ke makwabtaka da Kalgo.

An yi nadin ne a fadar Dan Galadiman Kalgo da misalin karfe 11:00 na safe,inda Uban kasar ya yi wa sabon Hakimin nasiha akan ya rike amana kuma yayi adalci a cikin shugabancinsa.

Sabon hakimin Alh.Bube ya shaida wa ISYAKU.COM cewa yayi matukar farin ciki da wannan nadin wanda ya gada daga Kakansa zuwa Mahaifinsa da Allah ya karbi ransa watannin baya a yau kuma ya gaji Mahaifin nasa a bisa wannan mukamin.

'Yan uwa da abokan arziki sun halara a wajen bikin nadin wanda Makadan gargajiya suka sheka kidi da bushe bushen Algaita.

Daga bisani daruruwan jama'a sun raka Hakimin zuwa garin nashi Garin Saini inda yake karbar gaisuwa da fatar alhairi daga Abokan arziki.Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN