• Labaran yau

  Yadda aka daura Auren 'yan Luwadi Musulmi a Ingila | isyaku.com

  An yi bikin daurin aure a tsakanin wasu matasa biyu Musulmi 'yan luwadi a Walsall na kasar Ingila.Shi dai Ango Jahed Chaundhuri 23,da Amaryasa Sean Rogan 19 sun daura Auren ne a dakin rijistan daurin Aure na Walsall.

  Bayanai sun nuna cewa yan luwadin sun kasance cikin soyayya fiye da shekara biyu kafin su yanke shawaran daura aure a tsakaninsu.

  Express & Star ta ruwaito cewa shi Ango Chaundhuri sanannen dan luwadi ne da yake harkokinsa a bayyane ba tare da kunya ko shakkar kowa ba.


  Bikin wanda aka gudanar bai sami halartar iyayensu ba amma sun kasance a cikin shiga irin ta gargajiya ta Sherwanis mai kalan zinari.

  Wannan shine karon farko a tarihin kasar Ingila inda aka sami daurin Aure na yan luwadi Musulmi.

  Dukkannin yan luwadin dai yan kasar Bangladesh ne.

  Ango Chaundhuri yace yana son ya shaida wa Duniya cewa "zaka iya zama dan luwadi amma kuma kai Musulmi ne tunda abinda kake yi bai shafi kowa ba".  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Yadda aka daura Auren 'yan Luwadi Musulmi a Ingila | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama