• Labaran yau

  DSS ta dakile shirin kai hare haren ta'addanci a ranar Sallah

  Hukumar binciken sirri ta ta Najeriya DSS, ta sanar da samun nasarar damke wasu ‘yan ta’adda da ke shirya kai jerin hare hare a garuruwan Sakkwato, Kano, Kaduna da kuma Maiduguri, yayin da ake bukukuwan Sallah karama.
  Jami’an hukumar sun kame biyu daga cikin wadanda ake zargin, Yusuf Adamu da Abdumuminu Haladu da safiyar wannan Juma’a a garin Sakkwato, kamar yadda jaridar Premium Times da ake wallafata a Najeriya ta rawaito.

  Cikin sanarwar da ya fitar a Juma’ar nan, kakakin hukumar ta DSS Tony Opuiyo, ya ce tun a makwannin da suka gabata suka samu bayannan sirri da ke cewa, ‘yan ta’addan na shirin kai hare haren bam a sassan Najeriya.

  A ranar 20 ga watan Yunin da muke ciki, hukumar binciken sirrin ta kama wani kwararre wajen hada bama bamai, mai suna Bashir Mohammed a Shekar Madaki da ke karamar hukumar Kumbotso jihar Kano.

  Yayin gudanar da bincike kuma jami’an na DSS sun gano manyan bindigogi kirar AK 47 guda takwas, bindigogi masu sarrafa kansu 20, bama-baman gurneti 27, sai kuma alburusai 793.

  Zalika jami’an sun kwace tukunyar gas guda, komfutar laptop 3, sai kuma, mota daya da babur din hawa.
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.

  Daga shafin RFI
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: DSS ta dakile shirin kai hare haren ta'addanci a ranar Sallah Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama