• Labaran yau

  Dan kunar bakin wake ya kashe mutum 16 a kauyen Borno | isyaku.com

  Mutum 16 ne ake fargaban sun mutu sakamakon wani kunar bakin wake da aka kai a kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Dolarai a kauyen Kofa da ke kusa da birnin Maiduguri.

  TheGuardian ta ruwaito cewa mai magana da yawun hukumar bayar da taimako na gaggawa NEMA a jihar Borno Abdulkadir Ibrahim ya shaida masu cewa da misalin karfe 8:45 na yammacin Lahadi wasu 'yan kunar bakin wake 'yan mata guda biyu suka yi kokarin kai harin,amma jami'an tsaro suka dakile yunkurin nasu.

  Abdulkadir ya kara da cewa wasu 'yan kunar bakin waken sun yi sa'ar tayar da bam da ke a jikin su a daya bangaren sansanin na 'yan gudun hijira wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutum 16 nan take.

  Kungiyar Boko Haram ta sha kai irin wadannan hare haren musamman a sansanin 'yan gudun hijira da makarantu a wannan yankin da lamurran kasuwanci ya gamu da koma baya sakamakon hare haren na 'yan kungiyar ta Boko Haram.
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Dan kunar bakin wake ya kashe mutum 16 a kauyen Borno | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama