• Labaran yau

  Shehu Sani: Shugaba Buhari na nan da ransa | isyaku.com

  Fadar shugaban kasa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yi a kan mutuwar Shugaba Muhammadu Buhari, ta na mai bayyana lamarin a matsayin wata manakisa domin a sanya fargaba a zukatan ‘yan Nijeriya.

  Mai taimka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu ya bayyana haka a shafin san a Twitter, inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya cewa, duk wanda ya samu wani bayani a yanar gizo to kada ya yarda da shi, domin karya ce kawai aka shirya don sanya fargaba a zukatan al’umma.

  Garba Shehu, ya ce babu wani abu da ya sami shugaba Muhammadu Buhari, don haka ya ce babu dalilin da zai sa mutane su shiga damuwa.

  Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar yada labarai Femi Adesina, ya ce babu abin da zai samu shugaba Buhari sai abin da Allah ya kaddara ma shi, ya na mai mika godiya ga duk masu yi wa Shugaba Muhammadu Buhari addu’o’i da fatan alheri.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

  Wannan labarin ya fara bayyana a shafin Liberty.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Shehu Sani: Shugaba Buhari na nan da ransa | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama