• Labaran yau

  Masarautar Yauri: An nada Sakataren Gwamnatin Kebbi Babale Umar "Fagacin Yauri"

  A ranar Asabar da ta gabata mai Martaba Sarkin Yauri Alh.Zayyanu Muhammed ya nada babban Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi Alh.Babale Umar a matsayin "Fagacin Yauri" a wani biki da aka gudanar na nadin a Fadar Sarkin na Yauri wanda ya sami halarcin Mataimakin Gwamnan jihar ta Kebbi Alh.Samaila Dabai Yombe.

  Mai Martaba sarkin Yauri yayi bayani cewa nadin na Sakataren Gwamnatin ya biyo bayan irin namijin kokari ne da gudunmawa da yake bayarwa wajen ci gaban Masarautar ta Yauri tare da la'akari da harkokin ci gaba da zaman lafiya.

  Sarkin ya kara da cewa al'adar Masarautar ta Yauri ne ta nada duk fitaccen dan Masarautar da ya kawo ci gaba da zaman lafiya a Masarautar.A nashi jawabi sabon Fagacin Yauri Alh.Babale Umar ya yi alkawari akan cewa zai yi ayyuka da zasu kawo cigaba a Masarautar ta Yauri ta hanyar yin koyi da mahaifinsa Mal.Umaru.

  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

  Hoto: Gettyimages

  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Masarautar Yauri: An nada Sakataren Gwamnatin Kebbi Babale Umar "Fagacin Yauri" Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama