• Labaran yau

  kebbi kwallon kafa: Sakaba united ta ci Zara united 2-1

  Sakamakon wasan kwallon kafa na zagaye kusa da na karshe (semi final) kungiyar kwallon kafa ta Sakaba united tayi nassarar doke takwararta ta Zara united ta hanyar zura kwallaye 2 ita kuwa Zara united tana da ci 1 a wasan da aka buga a jiya Asabar a babban filin wasa na jiha da ke sakatariyar Haliru Abdu a garin Birnin kebbi.

  Hamza Na Malgwai lamba 9 daga Zara united shine ya fara zura kwallo a ragar Sakaba united wanda daga bisani yan'wasan Sakaba united suka rama har da zarcewa.Yanayin da aka buga wasan kwallon kafar ya tabbatar da inganci da tsari a yadda mahukuntar harkar wasan kwallon kafa ta jihar Kebbi ke tafiyar da lamarin wasan na kwallon Kafa.

  Mal.Mustapha Umar sakataren kungiyar wasan kwallon kafa na jihar Kebbi ya shaida wa ISYAKU.COM cewa sun fara wannan gasar ne tun 20 ga watan Afrilu 2017 har izuwa yau 30 ga watan Afrilu inda suka kawo zagaye kusa da na karshe (semi final) kuma a halin yanzu suna buga wasan zagayen kusa da na karshe na biyu.

  Mustapha ya cigaba da cewa wasannin kwallon na federation cup kungiyar kwallon kafa ta Najeriya take shirya shi kuma ba wai wani babban tallafi take samu ba face idan an kai karshe wadanda zasu je su wakilci jihar Kebbi a mataki na kasa ita hukumar kwallon kafa takan tura wa Gwamnati ita kuma Gwamnati tana taimakawa kungiyoyin da suka yi nassara na 1 da na 2 da zasu wakilci jihar Kebbi a mataki na kasa.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: kebbi kwallon kafa: Sakaba united ta ci Zara united 2-1 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });