• Labaran yau

  Wani mutum ya daure Matar shi da janareto daga dare zuwa safe

  Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta kama wani mutum mai suna Ifeanyi Ajaero dan shekara 37 wanda ya daure matarsa da janareto daga dare har zuwa safe.Ifeanyi ya daure matarshi mai suna Obiageli mai shekara 28 ne daga daren Juma'a 14 zuwa ranar Asabar 15 ga wan Afrilu.

  Ifeanyi ya shaida wa 'yan sanda cewa ya daure matar tashi da janareto amma yayi haka ne domin ya kare kanshi.PM News ta ruwaito cewa kwamishinan 'yan sandan jihar Ogun Ahmed Iliyasu ya tabbatar da kama Ifeanyi akan aikata wannan laifin ya kuma yi gargadi cewa rundunar 'yan sanda ta jihar Ogun ba zata lamunci ayyukan tashin hankali a cikin gidajen aure ba.

  Kwamishin 'yan sanda Ahmed ya tura matsalar zuwa sashen bincike da abin ya shafa na rundunar 'yan sandan jihar domin ci gaba da bincike.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Wani mutum ya daure Matar shi da janareto daga dare zuwa safe Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama