Nasarar Macron ta sauya tarihin siyasar Faransa

Nasarar da Emmanuel Macron ya samu a zagayen farko na zaben shugabancin Faransa da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata, ya kawo karshen mamaye siyasar kasar da jam’iyyun Socialist da Republican suka yi.
Bayan tabbata da ta yi cewa yanzu Macron da Marine Le Pen ne zasu fafata a zaben shugabancin Faransa a zagaye na biyu da za’a yi a ranar 7 ga watan Mayu mai zuwa, Faransawa na cigaba da tofa albarkacin bakinsu kan yadda sakamakon zagayen farko na zaben shugabancin kasar ya kaya, ganin jam’iyyun da suka saba taka rawar gani a zaben kasar basu kai labari ba.
Karo na farko kenan a tarihin zaben kasar Faransa cikin shekaru 60, da ‘yan takarar jam’iyyun Socialist da Republican suka gaza kai labari.
Sakamakon wucin gadi ya nuna cewar Emmanuel Macron ya samu kusan kashi 24 na kuri’un zaben da aka yi jiya, yayinda Marine Le Pen ta samu sama da kashi 21.
Yayinda yake jawabi ga magoya bayansa, bayan nasarar da ya samu, Macron mai shekaru 39 ya ce ya dade yana bibiyar bukatun neman sauyi da Faransawa ke bayyanawa, wadda kuma ya gani a aikace yayin kada kuri’un da al’ummar kasar suka yi a zagayen farko na zaben shugabancin kasar.
Ita kuwa Marine le Pen yayin nata jawabin, cewa ta yi an tsallake katangar farko, a yanzu ne kuma za’a fara gwagwarmayar karbar iko.
Masu sa ‘ido kan siyasar Faransa na kallon Macron a matsayin wanda zai iya lashe zaben kasar idana aka fafata a zagaye na biyu.
Tuni dai manyan ‘yan takarar da suka fafata musamman suka bayyana goyon bayansu ga takarar Macron, inda suka ce samun nasarar Marine Le Pen hadari ne matuka ga kasar Faransa.

@ISYAKUWEB KU BIYO MU A SHAFIN MU NA FACEBOOK

  Nasarar Macron ta sauya tarihin siyasar Faransa ya fara bayyana ne a RFI

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN