• Labaran yau

  Dan tasha ya ci zarafin jami'in FRSC

  Wulakanci ne ga Gwamnatin Najeriya
  Wasu matasa da ake zargi da cewa zauna gari banza ne suka lallasa wani jami'in hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC a garin Nnewi da ke jihar Anambara a ranar Juma'a da ta gabata.

  A wani hoto da ya bayyana a shafin yanan gizo na naij.com,an gan wani matashi ya cukunkume wani jami'in hukumar ta FRSC a yayin da jami'in ke cikin damararsa ta aiki.

  Labarai masu karo da juna sun zargi jami'in da yunkurin karbar na goro daga wani mai babur wanda shi kuma ya harzuka ya kuma fada wa ma'aikacin da duka.

  Amma a wani jawabi da hukumar ta fitar wa manema labaru ta ce babu gaskiya a zargin da ake yi wa jami'an hukumar akan wannan lamarin,ta kara da cewa gaskiyar labarin shine wani dan acaba ne ya juya a yayin da yake kokarin ya tsere saboda ya hango jami'an hukumar da ke sintiri akan hanya domin duba ababen hawa.Garin hakan ne dan acaban ya fadi,lamarin da ya janyo hankalin zauna gari banzan da suka zo suka yi amfani da wannan dama suka ci zarafin jami'in na hukumar.
  Babu wanda zai wulakanta jami'i a wannan yanayi


  SHARHI

  Ta la'akari da irin abubuwan da ke faruwa da jami'an na FRSC a yayin da suke gudanar da ayyukan su akan titunan Najeriya musamman yadda wasu masu amfani da ababen hawa ke wulakanta jami'an wani lokaci ma har da barazana ga lafiya da rayukan jami'an wanda suke gudanar da aikin su domin kasarsu Najeriya.

  A jihar Kebbi a 'yan makonnin baya,an zargi wani direban motar haya da kashe wani jami'in hukumar ta FRSC da gangan ta hanyar bugeshi da motar haya da ya tuko kuma lamarin da yayi sanadin mutuwar jami'in nan take,shi kuma direban ya ki tsayawa lamarin da ya sa aka yi ta gudun famfalaki da shi amma sai a garin Kalgo kilomita 13 daga inda abin ya faru aka kamashi.

  Duk da yake akwai korafe korafe da yawa akan yadda wasu jami'an hukumar ke gudanar da ayyukan su amma ka'idar aikin hukumar shi ya haifar da wannan tunanin.

  Ya zama wajibi Gwamnati ta ba jami'an hukumar ta FRSC bindigogi domin su tafiyar da aikin su cikin mutunci da martaba da ya cancanci kowane ma'aikaci mai damara.Saboda aikin da suke gudanarwa ai don Gwamnati ne,kuma tunda dan tasha zauna gari banza zai cukunkume ma'aikacin Gwamnatin Najeriya mai kakin unifom kamar ya kamo kare kuma ba abin da ya faru,tau lallai wulakancin zai kai ga manyan jami'an hukumar kenan idan Gwamnati ta bari irin wannan lamarin na ci gaba da faruwa kuma babu wani mataki da aka dauka a hukumance.

  Isyaku Garba -Mawallafi

  @isyakuweb   ku biyo mu a shafin mu na Facebook

  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Dan tasha ya ci zarafin jami'in FRSC Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });