• Labaran yau

  Dan kasuwa ya maka su Saraki Kotu akan tantance Magu

  Wani kasurgumin dan kasuwa mazaunin Lagos Raji Rasheed Oyewumi, ya maka shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da wasu sanatoci kotu a kan rawar da su ka taka wajen tantance Ibrahim Magu a ranar 15 ga watan Maris da ya gabata.

  Dan kasuwar dai, ya bukaci kotu ta soke sakamakon da majalisar dattawan ta fitar dangane da matsayin Ibrahim Magu.

  Oyewunmi ya kuma bukacin kotun ta haramta wa Bukola Saraki da wasu ‘yan majalisa 10 halartar zaman tantance Magu nan gaba, domin a cewar sa, ba za su yi ma shi adalci ba a matsayin wandanda ke fuskantar tuhume-tuhume a hukuamar yaki da cin hanci da rashawa.

  ‘Yan majalisar da aka yi karar kuwa sun hada da Godswill Akpabio, da Jonah Jang, da Aliyu Magatakarda Wamako, da Stella Oduah, da Theodore Orji, da Rabi’u Musa Kwankwaso, da Ahmed Sani Yeriman Bakura, da Danjuma Goje, da Josua Dariye, da kuma Adamu Abdullahi.


  Liberty

  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Dan kasuwa ya maka su Saraki Kotu akan tantance Magu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama