• Labaran yau

  Jihar Kebbi ta bayar da tallafin N9,450,000 ga yara da suka koyi sana'a

  An yaye wasu dalibai wadanda suka koyi sana'a kala kala karkashin wata kungiya na taimakon kai da kai karkashin jagorancin Muhammed Bello a harabar babban Makarantar sakandaren jeka ka dawo na Gwamnati da ke Tudun wada a garin Birnin kebbi wanda ya sami halartar mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu da wasu manyan jami'an Gwamnatinsa.

  Yara Maza da Mata ne suka koyi sana'oi wadanda suka hada da yin takalma,yin cin cin,kayakin sawa na yara,da sauran su.Wasu daga cikin wadanda aka yaye sun bukaci Gwamnati ta kawo masu tallafi saboda amfani da suka ce shirin ke dauke da shi domin a yanzu haka sun sami sana'ar yi illa kawai suna bukatar tallafi domin su ci gaba da sarrafa sana'ar da suka koya.

  Manyan jami'an Gwamnati da ke wajen taron sun bayar da tallafi na kudi wanda Maigirma Gwamna Atiku Bagudu ya kammala ta hanyar bayar da N500,000 a madadin kowane dan Majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Kebbi ta tsakiya.Haka kuma Gwamnan ya bayar da tallafin Naira miliyan 5,450,000 jimillar kudin tallfi ga kungiyar sun kama N9,450,000.

  Gwamna Atiku Bagudu ya bukaci jama'a su hada kansu waje daya musamman Mata,ya kara da cewa "Muddin mata suka hada kansu dole ne su jawo hankalin kowane dan siyasa kuma zasu fi samun biyan bukata a kungiyance" ya kuma kara bayani akan cewa Gwamnatin sa a shirye take ta taimaka wa al'ummar da ta hada kanta domin samun ci gaban kansu.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Jihar Kebbi ta bayar da tallafin N9,450,000 ga yara da suka koyi sana'a Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });