Hafsoshin da abin ya shafa sun hada da CP Peter Yeni Tenkwa, da DCP Abubakar Abaka da kuma SP John Bukar.A cikin wata sanarwa, wani daraktan kwamitin Mista Sunday Dan Ogu, ya ce an dakatar da jami'an ne sai an kammala dukkan bincike a kan batun.Kawo yanzu babu tabbas kan abin da zai faru ga Mista Ngelari.
Ana zargin Hafsoshin da laifin hada baki domin a bada rahotu akan rashin lafiyar Ngileri ba bisa ka'ida ba wanda hakan yayi sanadin sakin daurarren tsohon Gwamnan.Rahotun ya nuna cewa rashin lafiyar Ngileri ya tsananta a yayin da yake daure a gidan yari,kuma Asibitin gidan yarin na Yola ba zai iya bayarda kulawa da ya cancanta ba ga tsohon Gwamnan.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
Tags:
LABARI