Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Ali Ndume har tsawon wata 6

Majalisar Dattijai ta Najeriya ta dakatar da Sanata Ali Ndume har tsawon wata 6,wannan ya biyo bayan dambaruwar da akayi ta takawa ne tsakanin Ali Ndume da wasu 'yan majalisar dattijai akan furucin da Ndume yayi ta nuna bukatar cewa a binciki shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Dino Malaye wanda dukkannin sanatocin suna fuskantar bincike daga wasu hukumomi na Najeriya akan aikata ba daidai ba.

Wannan matakain ya biyo bayan amincewa da majalisar dattawar tayi ne da sakamakon rahotu da kwamiti kan da'a ta gabatar ranar Laraba ta hannun shugaban kwamitin Samuel Anyanwu inda ta bukaci a dakatar da Ndume har tsawon shekara 1 amma majalisar ta sauya hukuncin zuwa dakatarwa ta wata 6.

Amma a yayin da ya bayyana a gaban kwamitin bincike,Ndume yace shi bai rubuta wata takardar baiyana laifi ko neman bincike ba akan sanatocin,yace yayi furucine akan ra'ayin kansa bayan ya karanta zarge-zargen da ake yi wa sanatocin a jaridu.


@isyakuweb--Shafin mu na Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb
Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN