• Labaran yau

  'Yan Sanda sun hana zanga-zanga da mawaki TuFace ya shirya a Lagos da Abuja

   Rundunar ‘yan Sanda a Najeriya ta haramta zanga-zangan nuna kyamar Gwamnati da wani mawaki ya shirya yi gobe lahadi da jibi Littini a biranen Lagos da Abuja.
  Kakakin Rundunar ‘yan sandan Jimoh Moshood ya fadi cikin wata sanarwa cewa sun sami bayanan sirri dake nuna zanga-zangan nuna kyamar Gwamnatin Muhammadu Buhari da mawakin Innocent Idibia da aka fi sani da TuFace  zai jagoranta akwai hadari.
  Shi dai wannan mawaki ya sanar da shirya zanga-zangan ne saboda Gwamnatin yanzu ta ki yin komi gameda halin matsi da ake fama dashi.
  Kungiyoyin dake rajin kare democradiyya dai sun nuna za su shiga wannan zanga-zanga a fadin kasar.
  A cewar Rundunar ‘yan sanda akwai wasu rahotanni dake nuna wata kungiya na shirya nata zanga-zangan don nuna goyon bayan Gwamnati a lokacin da wanda TuFace ya shirya na si.
  Wasu kafofin yada labarai a Najeriya sun ce TuFace ya ce za su gudanar da zanga-zangan duk da gargadin da aka yi masu.
  (RFI )
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: 'Yan Sanda sun hana zanga-zanga da mawaki TuFace ya shirya a Lagos da Abuja Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama