Header Ads

Yadda ta kasance da wanda ake zargi da Luwadi

Idan kuna biye da wannan shafin tun ranar Alhamis da ya gabata,na rubuto yadda ta kasance da wani Hamisu daga jihar Sokoto wanda ya yi yunkurin yin Luwadi da wani yaro a Nassarawa 2 da ke nan garin Birnin kebbi.Ina zaton ba laifi akan yin wannan bayanin don jama'a da ke da yara kewaye da wannan anguwan su kiyaye domin kada wannan la'anannen mugu da ahalin sa wadanda basu bayyana ba amma suna tare da shi su ci gaba da rusa darajar yara da mutuncin su ba tare da sanin iyayen su ba.

Bayan da aka gabatar da shi a gaban hukumar 'yansanda kuma ya amsa laifin yunkurin yin lalata da dan karamin yaro,hukumar 'yan sanda ta bada bilin shi saboda dama can yayi fitsari da kashi a yayin da ya sha duka kafin a zo da shi wajen 'yan sanda,saboda haka aka ba da belin sa.Ranar juma'a shi wannan Hamisu ya sake dawowa a wannan anguwan,inda ya sadu da wasu kananan mutane marasa wadataccen ilimin zamani da tsararren lissafin zaman duniya a bisa manufar ilimin fahimta,a cikin su akwai wadanda watakila su ne ahalin aikata wannan danyen aikin,ko kuma munafukai ne makiya gaskiya da tsarin su ya bayyana na rashin amana da son gaskiya,abin da muka ji daga baya shi ne wai an yi ma Hamisu kazafi ne.

Shin don Allah wanda baya wurin da aka binciki Hamisu yana da hurumin yin sharhi akan lamarin?..kusan mutum 50 ne suke wajen,kuma akalla akwai mutum 20 kewaye da shi a yayin wannan binciken tambayoyi da aka yi wa Hamisu.Akwai nadaddar muryar sa da bidiyo inda yake bayani da kan sa.Kuma kun lura  da hannun sa na dama dauke da raunin cizon da yaron yayi masa har sau hudu a wurare daban daban azabar da ya sa ala tilas ya saki yaron saboda cizo da ihu da yaron yayi ta yi,kuma ya zo ya gaya wa mahaifin sa wanda shi ya haifar da wannan bincike akan Hamisu ?.

Da farko Hamisu ya ce ya aikata lalata da yaron,a yayin da ake yi masa tambayoyi,daga bisani ya canja zancen inda yace Wallahi Tallahi bai aikata ba amma ya yi yunkurin yi,da 'yan sanda suka tambaye shi cewa don me ya sa yace ya aikata lalatar ta da yaron sai ya gaya masu cewa wanda ya koya masa Luwadin shine ya gargade shi akan cewa duk ranar da rana ta bacen dubu ya cika, idan ana dukan sa kuma aka tambaye shi ko ya aikata ..tau sai yace eh ya aikata,hakan zai sa wasu su bukaci a daina dukan sa domin a kai shi wajen jami'an tsaro,amma idan ya ce bai aikata ba to jama'a za su kashe shi.Hamisu ya ce wannan shi ne dalilin da ya sa ya ce ya aikata,amma ya ce Wallahi Tallahi bai aikata ba.Domin yaron ya ciccije shi kuma ya yi ta yin ihu wanda ya sa ala tilas ya kubuta,ya kuma sheka ya gaya wa Mahaifin sa.

Kuna sane da cewa a ranar Talata 14/2/2017 Hamisu ya sa 'yan sanda sun tsare wanda ya karbe shi beli na takaitaccen lokaci domin yayi yunkurin tserewa,ala tilas wanda ya karbe shi beli ya tsara yadda za'a kamo shi sa annan shi ya tsira sanadin hakan ya sa ya rubuta wa DPO takardar jaye hannun sa daga tsaya wa Hamisu?

Bayan da aka shiga Kotu,kuna sane da cewa Hamisu ya fakaici idanun jama'a sai ya sulale kana ya arce da gudu sai da aka yi masa kuwar barawo kuma dan sanda mai gabatar da kara ya tari babur kafin ya sami kamo Hamisu inda aka dawo da shi kotu da ankwa a hannayen sa?..a cikin munafukan da suka ce an yi mashi kazafi ne ba a gan ko mutum daya ba a Kotu.

Mai gabatar da kara kofur Faruku ya karanta wa Hamisu laifin da ake tuhumar sa da aikatawa a madadin Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kebbi a gaban Alkali,kuma Hamisu ya amsa laifin sa,ya kuma nemi Kotu ta yi masa sassauci.To don Allah jama'a idan dai mutum ba dan uwan Hamisu bane wajen aikata Luwadi da lalata kananan yara ta yaya za ka ce kazafi ne aka yi? ma'ana duk ilimin jami'an tsaro da suka gudanar da bincike da na Kotu da ta saurari karar ya zama kuskure kenan sai naku harsashe na rashi basira da lissafi ?
Powered by Blogger.