• Labaran yau

  Ya kashe Matar shi,Ya sassare ta guntu-guntu  Hukumar ‘yan sanda ta jihar Lagas ta kama wani matashi mai suna Sakiru Bello dan shekara 36 a bisa zargin kashewa da sassare jikin matar sa Sharifat Bello uwar yara uku a ranar 13 ga watan Fabrairu 2017.

  Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Sikiru ya gaya wa ‘yan sanda cewa bai yi niyyar kasha Sharifat ba kuma bas hi ne ya kasha ta ba ya ce abin day a faru shine,ya kira matar tashi Sharifat a inda suka je bakin teku,a yayin da suke dawowa ne a kan babur sai wani mai mota ya buge su,lamarin da ya sa suka fadi kuma kan sharifat ya bugi kwalta.Ya ce bayan sun isa gida ne can da dare sai ta fara koken cewa kan ta yana ciwo,yace ya kasa kai ta Asibiti ne domin baya da kudi,kuma ba su shiri da Uwayen Sharifat, balle ya nemi taimako daga wajen su,a cikin wannan yanayin ne matar tashi Sharifat ta mutu da dare.

  A ci gaba da bayani ga ‘yan sanda,Sikiru ya ce bayan da ta mutu da dare,sai ya rude ya rasa yadda zai yi,can sai tunani ya zo masa akan cewa ya sassare ta ya sanya a cikin Ghana must go sai ya je ya binne ta a wani gini da ba’a kammala ba inda ya binne sassan jikin Sharifat a rami daban-daban.

  Mahaifin Sharifat ya ce bayan basu gan sharifat ba har na tsawon wani lokaci,sai suka tuntubi mijin nata Sikiru,amma basu gamsu da martanin day a bayar ba,akan haka ne suka garzaya zuwa rukuni na “B” na ‘yan sandan jihar Lagos inda suka fara binciken da ya kai ga kamo Sikiru a cikin garin Lagos bayan ya gaya wa surukan sa cewa yana Ibadan bayan sun tuntube shi a wayan salula.

  Har yanzu dai ‘yan sanda suna ci gaba da bincike akan wannan mummunar rashin imani,da zarar an gama bincike ‘yan sanda za su gabatar das hi a gaban Kuliya.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ya kashe Matar shi,Ya sassare ta guntu-guntu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });