• Labaran yau

  Tsoffin ‘Yan Sanda a Jahar Jigawa Sun Tsunduma Bara

  Kimanin tsofaffin ‘yan sanda 22 ne suka tsunduma bara a jahar Jigawa a sakamakon kwashe watanni 17 da suka yi da yin ritaya ba tare da an biyansu hakkokinsu na giratuti da fansho ba.
  A wani rahoto da jaridar Leadershi Hausa ta wallafa, ta bayyana cewa an yi watsi da wadannan tsoffin ‘yan sanda, ba tare da la’akari da shekaru 35 din da suka yi suna bautawa kasa ba, al’amarin da ya sa suka shiga halin kaka-ni-kayi.
  An zanta da wasu daga cikin mutanen kamar su Insifekta Abubakar Muhammed wanda ya bayyana cewa dole ce ta sanya cikin yanayin bara domin neman abinda zai ci tare da biyan kudin hayar gidan da suke zaune.
  Sai wani tsohon dan sanda mai suna Baba Musa wanda ya ce “dole in yi bara domin a halin yanzu an kori yarana daga makaranta su kimanin shida duk da cewar ba mu da abin da za mu ci.”
  Haka shima wani wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce “wallahi a halin yanzu tuni maigidan da nake zaune a ciki ya kori iyalina daga cikin gidan sakamakon gaza biyan kudin haya wadda hakan dole ya jefa ni cikin barace-barace domin karfinmu ya kare babu wadda zai dauke mu wani aiki”
  Tsoffin ‘yan sandan sun ce duk wani yunkurinsu na neman hakkin su daga hukumar ‘yan sanda da kuma kamfanin da ke da hakkin biyan su kudaden ya ci tura.
  An nemi jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jahar, SP Abdul Jinjiri ta wayar salula, inda ya bukaci a bashi lokaci ya yi bincike akan al’amarin. Sai dai har lokacin da aka wallafar rahotan ba a ji daga gare shi ba.
  MUJALLARMU
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tsoffin ‘Yan Sanda a Jahar Jigawa Sun Tsunduma Bara Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });