• Labaran yau

  Sojojin Nijeriya Na Gudu Su Bar Matan Da Suka Yi Wa Ciki a Borno

  Wani rahoto da kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP ya wallafa na nuna cewa wasu daga cikin sojojin Nijeriya na yi wa mata ciki a Borno, sannan su tafi su bar su a lokacin da wa’adin aikin su ya cika.
  Yawancin matan ma ba su sanin su na dauke da juna biyu har sai an dauke Sojojin daga jahar ta Borno.
  Kamfanin ya zanta da wasu daga cikin matan, inda suka bayyana cewa rayuwarsu ta shiga kunci.
  Ummi Hassan ‘yar shekaru 18 ta ce tana dauke da cikin watanni biyu aka dauke sojan da ya mata cikin zuwa Lagos kuma ya barta cikin wahala duk da suna magana a waya.
  Ummi ta ce abincin da ma za ta ci yana ma ta wahala.
  Sai kuma Kaltime Ari da Amina Muhammed da sojojin suka yi wa ciki kuma har suka haihu ba su yi ido da iyayen ‘ya’yan ba.
  Wasu daga cikin matan sun ce sai da ta kai ga sun koma yin bara domin su yi hidima da kansu da jariransu.
  A shekarar da ta gabata dai, kungiyar kare hakkin Dan Adam ta Human Right Watch ta fitar da wani rahoto da ke zargin sojoji da ‘Yan sanda da ‘Yan kato da gora da yi wa mata fyade a sansanonin ‘Yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, ta hanyar yi masu alkawarin aure ko abinci.
  ALUMMATA
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sojojin Nijeriya Na Gudu Su Bar Matan Da Suka Yi Wa Ciki a Borno Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });